17/02/2026
GIDAUNIYAR SARKIN KOKO MALAM MUSA FOUNDATION, TA KADDAMAR DA FARA RABON ABINCIN AZUMIN RAMADAN, WANDA TASABA DA YI DUK SHEKARA, A CIKIN WANNAN WATAN MAI DARAJA, DON SAUKAKAMA AL'UMMA WAJEN NEMAN ABINCI.
Shahararriyar Gidauniyar nan mai suna
Sarkin Koko Malam Musa Foundation, karkashin jagorancin Mai Girma Sarkin Koko, ALH. MOHAMMED BELLO KOKO II, da Mai girma Ciroman Koko, ALH. SHEHU MOHAMMED BELLO KOKO, ta kaddamar da rabon abincin azumin watan Ramadan, Wanda tasaba da yi duk shekara acikin wannan watan mai daraja, inda a yau talata 17/02/2026, anfara rabawa al'umma wannan abinci, domin saukaka musu wajen neman abinci acikin wannan watan mai daraja, duba da yanayin tsadar rayuwa, inda ankafara rabawa Malamai, Limamai, Hakimai da ke yankin Masarautar Koko.
Bisaga yadda wannan Gidauniyar ke rabon abincin duk shekara irin wannan watan, wagga shekarar, Shuwagabannin ta sun kara, fadada rabon abincin, ta yadda zai kara kai ga al'umma, inda sunka umurci duk wani hakimi dake karkashin Masarautar Koko, irin su Hakimin Tudu, Hakimin Firchin, Hakimin Bayara, Hakimin Dada, da Magajin Gari, da su je, su kara zakulo mabukata domin ganin abincin yakara kai garesu don a saukaka musu neman abinci a wannan watan mai daraja, a halin yanzu, za'a sake raba abincin a garkar Wadannan hakimai Kamar yadda ankayi shekarar da tagaba, bisaga sunayen mabukata da anka umurcesu s**ara zakulowa.
Za'a raba abincin ne zuwa ga:-
1. Marayu da Zaurunoni, Wadan da aka umurci hakimai su zakulo.
2. Limammai da Malamai
3. Al'ummar Garin Koko da kewaye
4. Al'ummar yankin Besse
5. Al'ummar yankin Maiyama
6. Al'ummar da ke cikin gundumomi goma sha biyu na yankin Koko-Besse (12 Wards).
7. Kungiyoyi
8. Musakai, Kamar Guragu, Makahi, da Kutare
9. Uwayen Kasar yankin Koko-Besse da Hakiman Masarautar Koko.
Bayan kuma wannan gidauniyar mai fafutuka kan al'umma, ta buda wajen bayar da abincin buda baki guda goma Sha hudu (14), ga al'ummar da ke tsakanin yankin Koko, Besse da kuma Maiyama, domin saukakamusu wajen neman abincin buda baki wanda takeyi duk shekara. A kowane wuri guda, za a ciyar da mutanen a kalla mutun dari (100) a kullum, mutane dubu daya da dari Hudu (1,400) kenan a kowace rana, har kwana 30 na Ramadan, inda jimlar mutanen da zasu ciyar ta k**a mutane dubu arba'in da biyu (42,000) a cikin wannan watan mai alfarma na Ramadan, inda gobe larba 18/02/2026, Daya ga watan na Ramadan.
Daga cikin abincin da suke ciyarwa a kowane mazauni, akwai:- Shinkafa/Kwai da Ruwan Sanyi da Kuma Kunu/Kosai da Ruwan Sanyi a kowace Rana.
Haka zalika wannan gidauniyar ta bude wasu wurare guda uku (3) a cikin Garin Birnin kebbi, Kamar yadda sunka sabayi duk Shekara don ciyar da Al'umma abincin buda baki, inda za'a ciyar da mutun 100 a kowane waje, mutun 300 kenan a rana, mutane 9000 kenan a watan azumin Ramadana. Daga cikin abincin da suke ciyarwa a kowane mazauni, akwai:- Shinkafa/Kwai da Ruwan Sanyi da Kuma Kunu/Kosai da Ruwan Sanyi a kowace Rana.
Al'umma sun nuna farincikin su, bisa ga wannan babbar gudummuwar da akabasu domin saukakamusu wajen neman abinci acikin wannan watan mai daraja. Samun irin wadannan Shuwagabanni na wannan Gidauniyar Mai fafutuka don nemo hanyoyin da zasu kawo sauki ga Al'umma, bakaramin baiwa bace ga al'ummar yankin, duba da irin gudummuwar da sukeba al'ummar su.
Muna rokon Allah ya sak**a wadannan Shuwagabanni da alkhairi Amin, Allah ya kara taimakon su, a duk inda suke, Allah kabiya musu bukatun su na alkhairi Amin.
Sarkin koko Malam Musa Foundation.
17_02_2026