05/09/2026
MASARAUTAR GIADE TA GABATAR DA HAWAN SALLAR GANI NA FARKO
Giade, Bauchi — 5 ga Satumba, 2026: Masarautar Giade ta gudanar da Hawan Sallar Gani na farko a tarihinta, ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Giade, Alh. Muhammad Sabo Abdulkadir.
Bikin ya gudana a fadar Masarautar Giade cikin yanayi na annashuwa, inda Hakimai, mahaya dawakai, sarakuna, manyan baƙi da dimbin al’umma s**a halarta.
Hawan ya nuna kyawawan al’adun gargajiya, tare da ƙara ƙarfafa zumunci, haɗin kai da raya al’adun Masarautar Giade.
Hoto himma photography