12/09/2026
🚨 KIRAN AGaji GA AL’UMMAR ANGUWAR PANTAMI MALAM KURI DAKE CIKIN JAHAR GOMBE
Transformer ɗin Anguwar Pantami Malam Kuri ya samu matsala, lamarin da ya jefa al’ummar wannan yanki cikin matsananciyar wahala.
Rashin wutar lantarki ya haifar da rashin ruwa, kuma al’umma na fuskantar wahala wajen samun ruwan sha da sauran abubuwan da s**a danganci rayuwar yau da kullum. Abin takaici ne ganin al’umma suna neman ruwa cikin wahala saboda matsalar wutar lantarki.
Muna kira ga masu ruwa da tsaki, ’yan siyasa, ’yan kasuwa, masu hannu da shuni, da duk wanda Allah Ya h**e masa hali, da su kawo ɗauki domin a gyara ko a maye gurbin wannan transformer.
Al’ummar Pantami Malam Kuri na neman agaji. 🙏
Duk wanda zai iya taimakawa, Allah Ya saka masa da alheri. Wannan ba batun siyasa kawai ba ne; batun rayuwar al’umma ne.
PANTAMI MALAM KURI — MUNA NEMAN TAIMAKO. 🤲🕯️