15/07/2026
Wata Babbar Kotun Tarayya ta Nijeriya da ke zama a Abuja ta ba da umarnin kwace kadarori 48 na din-din-din wadanda ke da alaka da tsohon Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari'a na kasar na baya-bayan nan, Abubakar Malami, wanda ke fuskantar zarge-zargen halatta kudaden haram.
Kotun, a cikin hukuncin da Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ta yanke ranar Alhamis ta bayyana cewa ya k**ata gwamnatin tarayya ta kwace wadannan kadarori na din-din-din, wadanda ake zargin an mallake su ne da kudaden da aka samu ta haramtacciyar hanyar.
Ta kuma bayyana cewa Malami, wanda ya rike mukamin Ministan Shari'a daga ranar 11 ga watan Nuwamba, 2015 zuwa 29 ga watan Mayu, 2023 a karkashin gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya gaza karyata zargin mai gamsarwa na cewa an mallaki kadarorin ne ta hanyar haramtattun ayyuka.
Wannan hukunci ya biyo bayan wata bukata ce da Hukumar Yaki da Hana Yi wa Tattalin Arziki Ta'annati (EFCC) ta shigar.
Kamar yadda EFCC ta bayyana, ana kyautata zargin cewa an mallaki kadarorin ne da kudaden da aka samu ta hanyar aikata laifuka, kuma kadarorin suna bazu ne a jihohi uku (Kebbi, Kano, da Kaduna) da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.