13/03/2024
Wani bawan Allah yayi wannan rubutu ranar 10/02/2015 Fatan Allah yasa yana raye yanzu munason muga mi zai sake rubutawa
DUNIYA:
In banda Goodluck da rashin iya lissafi, wai ace Azumi na nan tafe nan da 2 Months, amma ji yadda kayan abinci s**a ƙara kuɗi, ko wannan kadai ya isa mu kayar dashi a zaɓen da zamu yi nan da 1 week me zuwa duk da mun ji cewa wai zasu daga sai zuwa watan march
Yanzu fa 50kg foreign rice ya zama ₦11,000 daga ₦8,500 kuma loka ɗaya na foreign rice din ₦350 haba!...
Crate na kwai ya koma ₦750 daga ₦600, yanzu ko wane kwai ₦20 ya koma a madadin ₦15...
Kwandon tumatir ya koma ₦12,000 daga ₦9,500...
Ice fish da ake siyar da ko wanne babba guda daya akan ₦60 - ₦80 yanzu ya koma ₦110 Haba Goodluck...
Goran mangyada me cin 10ltr da ake siyar dashi a ₦2,800 yanzu ya koma ₦3,500...
Buhun jan wake da ake siyar dashi ₦15,000 yanzu ya koma ₦17,200...
Gwagwanin peak milk na gari da ake siyar dashi ₦650 ya koma ₦700...
Buhun gyada 50kg da ake siyar dashi ₦9,500 ya koma ₦11,800...
Taliya ko wacce kwara daya ta koma ₦90 daga ₦70...
Lemu ko wanne kwara daya ya koma ₦15 daga ₦10...
Ayaba kuma duk bunch guda ya koma ₦130 daga ₦80...
Ledan semovita ya koma ₦1,700 daga ₦1,450...
Lokan wake ya koma ₦350 daga ₦250...
Lokan gero ya koma ₦80 daga ₦65...
Masara duk loka daya ₦120 daga ₦100...
Buhun sugar ya koma ₦10,000 daga ₦8,000 kuma lokan sugar ya koma ₦280 daga ₦220
Goodluck must go... Nigeria sai Buhari