08/06/2026
DAGA LONDON ZUWA NIGERIA: SAƘON ZUMUNCI MAI GIRMA.
Malamanmu kenan daga London sun kammala da’awa,
suna shirin dawowa ƙasar Nigeria.
Wanda abu Islam yake cewa a tare dashi
Da Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum Hafizahillah
Da Dr Mansur Isah Yelwa Hafizahillah.
Yake cewa:
Bismillah Alhamdulillah,
gani nan ga shehunnaina.
Alhamdulillah anyi taro nan UK lafiya,
an je UK London, an je Birmingham.
Gashi Allah ya nuna mana ƙarshe kowa zai k**a hanyar shi.
Su zasu koma Nigeria, ni kuma zan koma back to Belgium,
Alhamdulillah.
Sheikh Guruntum Hafizahillah yace:
Allah ya saka da alkhairi,
Allah kuma ya sa karɓabbene a wajen Allah,
Allah ya karɓa mana, Allah ya bar zumunci,
Allah ya ƙara maka rayuwa da zurriyarka albarka,
Allah ya ƙara taimakonka wajen ɗauke-ɗauken nan.
Dr Mansur Isah Yelwa Hafizahillah kuma yace:
Abu Islam, abin da zan ce shi ne
wannan ‘yan uwantaka ta addini da akanta muka haɗu.
Ina tuna tun farkon haduwarmu,
mun zo muka same ku a Switzerland,
Kuma gashi yanzu har mun zama ‘yan uwa family ɗaya.
Iyaye ɗaya, zuciya ɗaya.
Muna fata wannan ‘yan uwantaka ta cigaba.
Duk wanda ba irin wannan abota ya yi ta hanyar Allah ba,
idan aka je ranar kiyama abotar ta wargaje.
Amma idan aka yi ta saboda Allah,
kuma akan hanya mai kyau, to za a ji daɗi a duniya.
Kuma mafi girma, idan aka haɗu a lahira,
Mu haɗu a Aljannah in sha Allah.
Abu Islam ya ce:
Ina kaunarku, ku kawo mana ziyara,
Mun kawo malam Guruntum ziyara
Sai dariya ta tashi 🤍
Abu Islam yace ga Bakin gemu,
Darin gemu, da tsaka-tsakiya…
Dr Mansur ya amsa da dariya:
Ni ma bakin gemu ne gaba ɗaya 😄
Sheikh Guruntum ya rufe da addu’a:
Allah ya saukemu lafiya,
Allah ya saka da alkhairi,
Allah ya saka da alkhairi.
Dr Mansur Isah Yelwa kuma ya ce:
Muna godiya ga dukkan waɗanda muka samesu a nan,
da mutanen London, da dukkan ‘yan uwa.
Babu abin da zamu ce sai Allah ya saka muku da alkhairi.
🤍 Wannan shi ne haɗuwar zukata saboda Allah
Ba siyasa ba, ba duniya ba, sai soyayyar addi