Secretary APC kano state

Secretary APC kano state Shafin wallafa labarai Wanda s**a shafi sakataren jama'iyyar APC alh Ibrahim zakari sarina da kuma jama'iyyar APC a matakin jahar kano

DAY 002DAGA OFFISHIN SAKATAREN JAM'IYYAR APC NA JIHAR KANOJAGORA ALH. IBRAHIM ZAKARI SARINAJagora Alh Ibrahim Zakari Sar...
19/02/2026

DAY 002
DAGA OFFISHIN SAKATAREN JAM'IYYAR APC NA JIHAR KANO
JAGORA ALH. IBRAHIM ZAKARI SARINA

Jagora Alh Ibrahim Zakari Sarina

🌙 FADAKARWA KAN RUKO DA IBADA A WATAN RAMADAN
Ya ku ‘yan uwa Musulmi, a wannan rana ta biyu na watan Ramadan, muna kara jaddada muhimmancin riko da ibada, tsarkake niyya, da dagewa wajen aikata alheri.

Allah MaÉ—aukakin Sarki yana cewa a cikin

Al-Qur’ani:
"Ya ku wadanda s**a yi imani! An wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta shi ga wadanda s**a gabace ku domin ku samu taqawa."
(Suratul Baqarah: 183)

Wannan aya tana nuna mana cewa manufar azumi ita ce samun taqawa, wato tsoron Allah da kiyaye dokokinsa a fili da boye.

Haka kuma, Manzon Allah ï·º ya ce:
"Duk wanda ya azumci Ramadan da imani da neman lada, an gafarta masa zunubansa da s**a gabata."
(Bukhari da Muslim s**a ruwaito)
Wannan hadisi yana karfafa mana guiwa da mu dage wajen:

Yin sallah akan lokaci
Karatun Al-Qur’ani
Yawaita istigfari
Ciyar da mabukata
Kyautata mu’amala da jama’a
Mu tuna cewa Ramadan wata ne na gyaran zuciya, yafiya da rahama.

Kada mu bari ranaku su wuce ba tare da cin gajiyar falalar wannan wata mai albarka ba.

Allah Ya ba mu ikon kammala azuminmu lafiya, Ya karbi ibadunmu, Ya sa mu cikin bayinsa na gari.
Amin Ya Rabbal Alamin.

Bashir Hamisu Danbaba
Jagora Alh Ibrahim Zakari Sarina

DAY(001) TAKAITACCEN FADAKARWA KAN AZUMIN WATAN RAMADANOfishin Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe ta Ƙasa Reshen Jihar Kano (P...
18/02/2026

DAY(001) TAKAITACCEN FADAKARWA KAN AZUMIN WATAN RAMADAN

Ofishin Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe ta Ƙasa Reshen Jihar Kano (Public Complaint Commission Kano State) ƙarƙashin jagorancin
Right Honourable Alh.Ibrahim Zakari Sarina

na kira ga daukacin al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan wata mai alfarma na Ramadan wajen ƙara kusanci ga Allah (SWT), da tsarkake zukata, da gyara halaye.

Azumin Ramadan ba kawai hana kai abinci da abin sha ba ne, illa wata makaranta ce ta tarbiyya, haƙuri, juriya da tausayi ga marasa galihu.

Ya kamata mu ƙara yawan ibada, karatun Alƙur’ani, sadaƙa, da nisantar duk wani abu da zai rage lada ko ya jawo fushin Allah.

Haka kuma muna jan hankalin jama’a da su kiyaye doka da oda, su zauna lafiya da juna, tare da kauce wa rikici da duk wani hali na cin zarafi ko tauye haƙƙin wasu.
Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya gafarta mana kura-kuranmu, Ya sa mu kasance cikin bayinsa na kwarai.

Office of the Public Complaint Commission
Kano State
Signed:
Bashir Hamisu Danbaba
Ibrahim Zakari Sarina

SAƘON BARKA DA SHIGA WATAN RAMADANDaga Ofishin Mai Girma Sakataren Jam’iyyar APC na Jihar KanoJagoran Siyasar Karamar Hu...
17/02/2026

SAƘON BARKA DA SHIGA WATAN RAMADAN

Daga Ofishin Mai Girma Sakataren Jam’iyyar APC na Jihar Kano
Jagoran Siyasar Karamar Hukumar Garko Ibrahim Zakari Sarina

Ina miƙa saƙon barka da shigowar watan Ramadan zuwa ga daukacin al’ummar Musulmin Najeriya baki ɗaya, musamman al’ummar Jihar Kano State.
Wannan wata mai alfarma wata ne da Allah (SWT) Ya kebance shi da rahama, gafara da kubuta daga wuta.

Wata ne na azumi, tsarkake zukata, yawaita ibada, da kusantar Ubangiji.

Allah Ya ja kunnen bayinsa da su riƙe azumi da gaskiya da tsoronSa, kamar yadda Ya ce a cikin Al-Qur’ani Mai Girma.

Ya ku waɗanda kuka yi imani! An farlanta azumi a kanku kamar yadda aka farlanta shi a kan waɗanda suke gabaninku, domin ku samu taƙawa.

A wannan wata, muna tunasar da al’umma da su.
Ƙara yawaita sallah da karatun Al-Qur’ani
Yin addu’o’i domin zaman lafiya da ci gaban ƙasa

Gujewa hassada, gulma, zagi da duk wani abu da zai rage ladan azumi
Taimakon marasa galihu da tausaya wa mabukata

Ramadan wata ne na haɗin kai da juna, yafiya da kyakkyawar mu’amala. Mu yi ƙoƙari mu gyara halayenmu, mu inganta zumunci, mu nemi gafarar Allah bisa kura-kuranmu.

Ina roƙon Allah (SWT) Ya ba mu ikon kammala wannan wata cikin koshin lafiya da imani, Ya karɓi ibadunmu, Ya gafarta mana zunubanmu, Ya kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.

Barka da Ramadan Allah Ya maimaita mana shi cikin alheri da yalwar arziki.
Wassalamu Alaikum Warahmatullah

Bashir Hamisu Danbaba
Sarkin Yakin Jagora
Alh Ibrahim Zakari Sarina

OFFICE OF THE COMMISSIONER PUBLIC COMPLAINT COMMISSIONER KANO STATE.A madadin Mai Girma Kwamishinan Hukumar Karɓar Koraf...
15/02/2026

OFFICE OF THE COMMISSIONER PUBLIC COMPLAINT COMMISSIONER KANO STATE.

A madadin Mai Girma Kwamishinan Hukumar Karɓar Korafe-korafe ta Ƙasa (PCC) reshen Jihar Kano, Jagora Alhaji Ibrahim Zakari Sarina,

muna miƙa saƙon jaje mai cike da alhini da jimami ga al’ummar Kasuwar Singa da ɗaukacin al’ummar Kano baki ɗaya, bisa iftila’in gobara da ya afku a ranar Asabar.

Wannan lamari babban rashi ne ga ‘yan kasuwa da iyalai da dama, inda dukiya da jari s**a salwanta.

Muna tausaya musu ƙwarai da gaske, tare da fatan Allah Ya ba su haƙuri da juriya a wannan mawuyacin hali.

Muna addu’a:
Ya Allah, Ka mayar musu da alheri fiye da abin da s**a rasa. Ka ba su juriyar wannan jarrabawa, Ka sauƙaƙa musu hanyoyin farfaɗowa da cigaba.

Ya Allah, Ka kiyaye gaba ɗaya al’ummar Kasuwar Singa da Jihar Kano daga irin wannan iftila’i a gaba. Ka tsare mu daga gobara, bala’o’i da duk wani sharri bayyane da ɓoyayye.

Ka sanya zaman lafiya, tsaro da wadata a tsakaninmu.

Haka nan muna kira ga hukumomi da al’umma da su ƙara ɗaukar matakan kariya da wayar da kai domin kauce wa maimaituwar irin wannan iftila’i nan gaba.
Allah Ya kiyaye gaba, Ya tsare dukiyoyinmu da rayukanmu. Ameen.

A madadin Mai Girma Kwamishinan PCC Reshen Jihar Kano
Jagora Alhaji Ibrahim Zakari Sarina

SAKON BARKA DA JUMA'AH.Ya Allah (SWT),Kai ne Mai iko da komai, Mai tsare Wannan Bawanaka daga dukkan sharri na bayyane d...
13/02/2026

SAKON BARKA DA JUMA'AH.

Ya Allah (SWT),
Kai ne Mai iko da komai, Mai tsare Wannan Bawanaka daga dukkan sharri na bayyane da boye.

Muna neman tsarinka daga sharrin makiya, daga hassada, daga cutarwa, da duk wani mummunan nufi da aka shirya akan sa.

Ya Allah, ka mayar da sharrinsu ya koma kansu, ka rusa duk wani shiri na cutarwa kafin ya iso gare shi.

Ka lullube shi da kariyarka, ka tsare shi da mala’ikunka, ka kare shi da sunayenka masu tsarki.

Ya Rabbana, duk wanda yake da nufin sharri a kansa, ko a iyalansa, ko a aikinsa
ka toshe masa hanya, ka dauke masa damuwa, ka bashi nasara a kansa ba tare da cutarwa ba.

Ka sanya shi cikin amincinka da tsarinka a ko wane lokaci.

Hasbunallahu wa ni’imal wakeel. Ni’iman Maula wa ni’iman Naseer Dubu Saba'in (70,000) Gaba Da Bayan Ka Jagoran mu Alh Jagora Alh Ibrahim Zakari Sarina

Allah Ya Baka Nasara A kan Masu Nufinka Da Sharri Albarkar Wannan Rana Ta Juma'ah 🤲

Barka Da juma'ah
Bashir Hamisu Danbaba
Sarkin Yakin Jagora Alh Ibrahim Zakari Sarina

Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Rajiun Hakika na kadu matuka da samun labarin mummunan kisan gillar da aka je har cikin gida...
19/01/2026

Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Rajiun

Hakika na kadu matuka da samun labarin mummunan kisan gillar da aka je har cikin gida aka yi wa matar aure tare da 'ya'yanta guda shida.

Tabbas wannan lamari abin tausayi ne kwarai, kuma abu ne da ya girgiza zukata tare da jefa firgici cikin al'umma.

A yayin da nake Allah-wadai da wannan mummunar ta'asa, ina kuma yabawa hukumomin tsaro bisa jajircewa da gaggawar da su ka nuna wajen ganin an bankado tare da cafke wadanda su ka aikata wannan aika-aika.

Ya zama wajibi a gare mu a matsayinmu na al'umma mu Kara sanya Ido a cikin unguwanninmu, mu kula da juna, domin kauce wa fadawa cikin komar bata-gari.

Na kuma kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da na shari'a da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an hukunta wadannan marasa imanin domin ya zama izina da kariya ga faruwar hakan anan gaba.

Ina mika ta'aziyya ta ga daukacin al'umar jihar Kano musamman ga mahaifin yaran da 'yan uwansu baki daya.

Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya jikan wadanda su ka rasu, ya sanya Aljannatuk Fidausi ta zamo makomarsu. Amin.

Hon Alh Ibrahim Zakari Sarina

ARMED REMEMBRANCE DAYCommemoration of National HeroesToday, we don't just remember we bow our heads in reverence to hono...
15/01/2026

ARMED REMEMBRANCE DAY
Commemoration of National Heroes

Today, we don't just remember we bow our heads in reverence to honor the heroes of the Nigerian Armed Forces, who gave their lives without hesitation for this nation to stand tall.

It is the blood of heroes that nourishes the Nigerian flag. Without their sacrifices, we wouldn't know the meaning of freedom, peace, and unity.

Hon. Alhaji Ibrahim Zakari Sarina Commissioner, Public Complaints Commission, Kano State, extends profound respect and immeasurable gratitude to the fallen heroes, emphasizing that they will never be forgotten not today, not tomorrow, nor forever. This day is proof that a nation doesn't stand with world it stands with courage, blood, and truth.

Therefore, it is the duty of every citizen to uphold what our heroes died for: justice, security, dignity, and unity. As Commissioner, Public Complaints Commission, Hon. Alhaji Ibrahim Zakari Sarina stands firm in defending the rights of the vulnerable, confronting oppression, and ensuring the values of our heroes' sacrifices are not in vain.

Honoring heroes is not just words it is action. Action of truth, justice, and patriotism.

Bashir Hamisu Danbaba

Sakataren Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Hon.Alh. Ibrahim Zakari Sarina  , ya ce har zuwa yanzu jam’iyyar ba ta da wata sa...
14/01/2026

Sakataren Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Hon.Alh. Ibrahim Zakari Sarina , ya ce har zuwa yanzu jam’iyyar ba ta da wata sahihiyar masaniya kan jita-jitar da ke yawo game da yiwuwar dawowar Gwamna Abba Kabir Yusuf cikin APC.

Hon. Sarina ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da Lumana Radio, inda ya ce kawo yanzu Gwamna Abba bai tuntubi shugabancin jam’iyyar APC a Kano ba dangane da batun sauya sheƙa.

Congratulations Distinguished Dr Barau I. Jibrin Maliya.Sakon Mai Girma Sakataren Jam'iyyar APC Na Jahar kano Alh Ibrahi...
07/01/2026

Congratulations Distinguished Dr Barau I. Jibrin Maliya.

Sakon Mai Girma Sakataren Jam'iyyar APC Na Jahar kano Alh Ibrahim Zakari Sarina

Mai Girma Sakataren Jam'iyyar APC Na Jahar Kuma Jagoran Siyasar Karamar Hukumar Garko Ibrahim Zakari Sarina  A matsayins...
06/01/2026

Mai Girma Sakataren Jam'iyyar APC Na Jahar Kuma Jagoran Siyasar Karamar Hukumar Garko Ibrahim Zakari Sarina

A matsayinsa na Sakataren Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Yana daukar shugabanci a matsayin amanar Allah da al’umma, ba wai matsayi na alfahari ba.

Jam’iyyar mu ta APC ta ginu ne bisa hadin kai, gaskiya, ladabi da bin doka, kuma wadannan su ne ginshikan tafiyarmu a kullum.

Yana girmama dukkan ‘yan jam’iyyar APC na Jihar Kano, tun daga manya har kanana, domin jam’iyya ba ta karfi sai da hadin kan ‘ya’yanta.

Kowa na da muhimmanci, kowa na da rawar da zai taka wajen ci gaban jam’iyya da Jihar Kano baki daya.

Saboda haka, kofa a bude take ga shawarwari, fahimtar juna da gina jam’iyya bisa adalci da mutunci.

Haka kuma, a matsayinsa Na Kwamishinan Public Complaints Commission a Jihar Kano, Yana daukar aikinsa da tsantsar gaskiya, adalci da jin tsoron Allah. Wannan hukuma ta na wakiltar muryar al’umma, kuma wajibi ne a saurari korafe-korafensu tare da neman mafita cikin lumana, doka da oda.

Manufarmu a bayyane take: gina jam’iyya mai karfi, tabbatar da adalci, da kuma hidima ga jama’a ba tare da nuna bangaranci ba.

Wannan ita ce siyasar dattako da jagoranci na gaskiya, wadda ke girmama kowa, tana kuma sanya muradun jama’a a gaba.

Dady Allah Ya baka ikon sauke wannan nauyi da aka dora maka, Ya kuma ci gaba da hada kan ‘yan APC da al’ummar Jihar Kano baki daya

Bashir Hamisu Danbaba

Alh Ibrahim Zakari Sarina  Jagora ne Tsayayye Kuma Mai Tsayuwa Da, aiki tuƙuru, Domin Tabbatuwar nasara mai ƙoƙarin Gask...
05/01/2026

Alh Ibrahim Zakari Sarina Jagora ne Tsayayye Kuma Mai Tsayuwa Da, aiki tuƙuru, Domin Tabbatuwar nasara mai ƙoƙarin Gaske Wajen Tsayar Da Gaskiya a Muhallinta

Mun haÉ—a Kaya Munyi niyya, mun É—aure zuciya Jagora Alh Ibrahim zakari Sarina a gaba, mu Kowa Zamu so a bayansa Yake ba sassauci, ba ja da baya!

Babu magana mai nauyi aiki ke nuna gaskiya Jagorancin Dady ya bayyana Nazari Da hangen nesa, tsayin daka A kan Hakkokin Al'umma

Duk inda ya dosa, mu muna tare da shi.

Duk ƙalubale, duk shakku ba zai tsayar da mu ba Duk Wuya Nan Shine Layin Mu Kuma Shine Ra'ayin mu Kuma Shine Matsayar Mu

Allah Ya Cigaba Da Tsare kimarka Da Martabar Ka Dady Allah Ya cika Maka Burin Ka Duniya Da kiyama

Muhammad Bashar Danbaba

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Secretary APC kano state posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category