Aminu Ibrahim Itas

Aminu Ibrahim Itas Revelutionary Comrade

28/11/2024

How To Start A Poultry Business Farming In Nigeria 👇

28/11/2024

Dangote announces petrol price cheaper than PH refinery amid strong competition.

11/04/2023

~For those who suffer in silence, I pray Allah eases your pain.

11/04/2023

May Allah grant us the best in this world and hereafter🤲.

03/04/2023

Ramadaniyyat: 1444 [3]

‘Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (3)

Ci gaba…..

Tasowarsa:

5. Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya ya taso a gidan ilimi; gidan da babu abin da s**a sa a gaba sai darasi da bincike da rubuce-rubuce da neman ilimi. Don haka ya sami kansa cikin wani yanayi mai cike da son ilimi da malamai da sanin mahimancin neman ilimi. Wannan yanayi ne ya yi wa Ibnu Taimiyya tasiri babba a rayuwarsa. Tun yana ƙarami ya haddace Alƙur’ani mai girma, ya kuma lizimci karatunsa da tilawarsa dare da rana, ya mayar da shi ya zama abokin hirarsa tun daga wannan lokaci har zuwa lokacin da aka tsare shi a kurkuku, ya zamanto ba shi da abin karatu sai Alƙur’ani. Kamar yadda masana tarihi s**a faɗa cewa, a zamansa na ƙarshe a kurkuku ya yi hatma (wato sauka) ta Alƙur’ni har sau tamanin.

6. Baya ga Alƙur’ani, Ibn Taimiyya ya mayar da hankali sosai a kan ilimin Hadisi, ya shiga nemansa gadan-gadan ba ji ba gani, musamman saboda kasancewar mahaifinsa Abdul-Halim shi ma babban malamin hadisi ne shararre a zamaninsa, domin kuwa isowarsa garin Dimashƙa ke da wuya, sai ga shi an ba shi babbar kujerar karantarwa irin wadda ake ba wa manyan malamai a garin, duba da yadda labarin zurfin iliminsa ya bayyana ya kuma watsu ko’ina a gari. An ba wa Mahaifin Ibnu Taimiyya kujerar karantawa a babban masallacin Banu Umayyah, (Al-Jami’ul Umawi) da ke birnin Dimashƙa. Sannan ya zama babban Shehin Makarantar Darul-Hadis As-Sukkariyya.

7. Mahaifin Ibnu Taimiyya, watau Shihabud-Din Abul Mahasin Abdul-Halim Al-Harrani, malami ne da aka yi wa shaida da zuzzurfan ilimi. Masana tarihi sun ce, yakan hau kujerar karantarwa ya yi ta zuba karatu da ka, na tsawon sa’o’i ba tare da yana riƙe da ko tsinke a hannunsa ba b***e kuma littafi. A hannu wannan bijimin Malami ne Ibnu Taimiyya ya taso, Allah kuma ya kimsa masa son ilimin hadisi da fiƙihun Hadisi, waɗannan fannoni biyu kowa su ne tushen ilimin addini.

Zamu cigaba insha Allah....
Copied From Prof Muhammad Sani Umar Prof Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo. (Fans Group)Prof Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo. (Fans Group)Prof Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo. (Fans Group)Prof Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo. (Fans Group)Prof Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo. (Fans Group)Prof Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo. (Fans Group)Prof Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo. (Fans Group)

02/04/2023

Ramadaniyyat: 1444 [2]

‘Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (2)

Ci gaba…..

4. Tarihi bai ba mu wani labari game da mahaifin Ibn Taimiyya ba, domin kuwa ya rasu a shekara ta 682 lokacin da Ibn Taimiyya yana matashi sosai bai wuce shekara ashirin da ɗaya ba. Amma mahaifiyarsa ta rayu har ta ga lokacin da ɗanta ya zama wani jan-gwarzo mai yaƙin ba wa sunnar Annabi (SAW) kariya da faɗa da bid’o’i da miyagun al’adu. Mahaifiyarsa ta ba shi gudunmawa da ƙarfin gwiwa a fafutukarsa da jihadinsa. Yayin da yake tsakiyar gwagwarmaya a fagen daga a ƙasar Masar, bayan kuma an kulle shi a gidan kaso, ya riƙa aika mata da wasiƙu masu cike da kalmomin nuna biyayya da girmamawa da kyautatawa, ya kuma riƙa ɓoye mata matsalolinsa da halin da ya tsinci kansa a ciki, domin kada ya jefa mata raɗaɗin rabuwa da shi.
Za mu ci gaba insha Allah…….

Copied From Prof Muhammad Sani Umar Rijiyar Prof Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo. (Fans Group)Prof Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo. (Fans Group)

01/04/2023

Ramadaniyyat: 1444 [1]

‘Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibn Taimiyya, Malami Na Allah (1)

1. A wani lokaci a cikin shekarar hijira ta 668, duk wani matafiyi daga garin Harran zuwa Dimashƙa na ƙasar Suriya (Syria), zai iya cin karo da wani magidanci tare da iyalansa tafe a kan wannan hanyar, domin tsira da rayuwarsu daga wani mummunan hari da ‘yan ta’addar Tatar s**a kai wa garinsu Harran, inda kuma yi ta’adi mai yawa na dukiya da rayukan jama’a. Wannan magidanci tare da iyalansa, sun k**a hanyarsu ta zuwa garin Dimashƙa suna jayen da amalanke mai dauke da wasu ‘yan kayayyakinsu da ba su taka kara sun karya ba. Tare da su kuma akwai wani ɗan karamin yaro da bai wuce shekara bakwai a duniya ba, amma kuma mai matuƙar kwazo da basira da hankali irin na manyan mutane. Wannan yaro ya buɗe ido ya ga irin ta’addanci ‘yan Tatar s**a tabka, sai wannan ya ƙara masa laƙantar gwagwarmaya da fadi-tashin rayuwa, domin a gaban idonsa ya ga yadda s**a tarwatsa komai a garinsu, s**a tilasta wa iyayensa fita gudun hijra da barin gidajen zamansu karfi da yaji. Wannan yaro shi ne: Abu Al-Abbas Taƙiyyuddin Ahmad ɗan Abdul-Halim ɗan Abdus-Salam ɗan Abdullahi ɗan Khudhairu ɗan Muhammad, wanda aka fi sanin ‘yan danginsa da suna: Iyalan ɗan Taimiyya.

2. An haifi Ibn Taimiyya ranar goma ga watan rabi’ul Auwal, a shekarar 661 bayan hijira. Wasu masana ma suna cewa, an haife shi ne ranar 12 ga Rabi’ul Auwal.

3. An yi saɓanin wajen tantance cewa shi Balarabe ne ko Bakurde ne, wato dan ƙabilar Kurdawa, to amma wannan ba wani abu ne mai muhimmanci babba ba, domin abin alfahari a wajen Ibn Taimiyya shi ne kyawawan ayyukansa da gwagwarmayar raya sunnar Manzon Allah (SAW) wanda ya kai shi ga mutuwa a cikin gidan kaso.
Zamuci gaba insha Allah..

01/04/2023

Hope is the cornerstone of our faith. Always have hope in the Almighty’s Mercy. Don’t let anyone tell you otherwise. Holding on to hope is your greatest strength. Use it to anchor you in times of crisis. The situation could always be worse. But he who has hope has everything.

Address

Kano

Telephone

+2349022351401

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Aminu Ibrahim Itas posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Aminu Ibrahim Itas:

Share