Abdulmaleek m star

Abdulmaleek m star Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Abdulmaleek m star, Photographer, Aduwa biyu shamaki world gombe, Lambe.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DARAJOJIN AHLUL BAITI:Hadisi daga Sayyidah Zainab 'Yar Abu Rafi'in Maulan Manzon Allah (S.A.W...
03/08/2025

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

DARAJOJIN AHLUL BAITI:

Hadisi daga Sayyidah Zainab 'Yar Abu Rafi'in Maulan Manzon Allah (S.A.W) tace :

"Naga Fadimatu (alaihas salam) 'Yar Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) tazo da 'ya'yanta guda biyu wajen Manzon Allah (S.A.W) alokacin da yake jinyarsa wacce aka karbi ransa acikinta.

Sai tace masa "Ya Ma'aikin Allah wadannan 'Ya'yanka ne. To (ina so) ka gadar dasu".

Sai yace "AMMA HASSAN TO NA BASHI KWARJININA DA HALAYEN SHUGABANCINA. AMMA HUSSAINI NA BASHI HALAYEN BAIWA IRIN NAWA DA KUMA JARUMTAKANA".

ADUBA :

- AL-ISABAH Ta Hafiz Ibn Hajr Al'asqalaniy, tarjamah ta 11238.

- USUDUL GHÃBAH NA IBNUL ATHEER (Tarjamah ta 6963).

- TAJREEDU ASMA'IS SAHABAH (Juz'i na 2 shafi na 272).

- IBNU ASAKIRA acikin Tareekh nasa, juzu'i na 4 shafi na 214 da na 414.

- ABU NU'AYM acikin Dala'ilun Nubuwwah.

- KANZUL 'UMMAL na Muntaqal Hindiy hadisi na 34,272. Kuma yace Tabaraniy ma ya ruwaitoshi acikin Mu'ujamul Kabeer da Ibnu Mundah da Ibnu Asakira dukkansu daga Nana Fatimah 'yar Manzon Rahama (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

QARIN BAYANI:

Hakika duk wanda ya karanci tarihin wadannan manyan Shugabannin zai tabbatar da cewa tabbas sun gaje halayen Kakansu (S.A.W) fiye da kowanne mahaluki aduniya.

Halayen Shugabanci da jagoranci irin na Imamu Hassan, koda ranar da ya hau kujerar Khalifanci bayan yayi Khutubah sai da ya bama jama'a za'bi. Yace musu "Idan kuna ganin ban chanchanta ba, zan sauka ku zabi duk wanda kuka ga yafi ni dacewa".

Sai s**a ce "Mu mun zabeka Ya 'dan Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

Sannan gashi da mutukar kwarjini irin nasu na Ahlul Baiti. Ga yawan murmushi da tawadhu'u da hakuri da juriya, ga kuma zurfin ilimi duk babu k**arsa.

Imamul Husaini shima ya gaje halin baiwa irin na Kakansa domin kuwa alokuta uku daban daban yana kyautar da dukkan abinda ya mallaka baki daya.

Kullum hannayensa cikin kyauta da kyautatawa suke. Bai ta'ba yin rowa ba.

Wajen jarumtaka kuwa,

🙏🏻😍❤️🔥📸
02/07/2025

🙏🏻😍❤️🔥📸

BISMILLAHIR RAHMANIR KU KARANTA KU QARU 🔘 Wanda ya fara yin azumi aduniya shine Annabi Adam (alaihis salam). Ya kasance ...
08/05/2025

BISMILLAHIR RAHMANIR

KU KARANTA KU QARU

🔘 Wanda ya fara yin azumi aduniya shine Annabi Adam (alaihis salam). Ya kasance yana azumtar kwanaki uku akowanne wata.

🔘 Mala'iku (alaihimus salam) sune s**a fara yin dawafi adakin Ka'abah tun kafin Annabi Adam (alaihis salam).

🔘 Wacce ta fara rasuwa daga cikin matayen Manzon Allah (S.A.W) abayansa ita ce Sayyidah Zainab bintu Jahash (ra). Kuma ita ce ta biyar acikin jerin matayen da ya zauna dasu a Madeenah.

🔘 Daga cikin matayen Manzon Allah (S.A.W) guda biyu ne ka'dai s**a rasu ahannunsa.

1. Nana Khdeejah bintu Khuwailid (ra) ta zauna dashi tsawon shekaru 25 ko 26 kafin rasuwarta.

2. Nana Zainab bintu Khuzaimah (ra) ta zauna dashi tsawon watanni shida ne kafin rasuwarta

🔘 Farkon Malamin da ya fara tarawa tare da rubuta hadisan Annabi (S.A.W) aduniya shine Imam Muhammad ibnu Shihab Azzuhriy (rah) wanda shi kuma almajirin Sahabbai ne. Kuma Imamu Malik yana daga cikin dalibansa.

🔘 Farkon wanda Annabi (S.A.W) ya na'dashi a muqamin Ameer (wato sarkin yaqi) shine Sayyiduna Abdullahi bn Jahshin Al Asadiy (ra).

🔘 Wanda ya fara zare takobi ya zubda jinin kafiri saboda ba da kariya ga Manzon Allah (S.A.W) shine Sayyiduna Sa'adu bn Abi Waqqas (ra).

Salatin Allah da amincinsa su tabbata bisa Fiyayyen Annabawa da Manzanni Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa masu albarka, da dukkan salihan bayi har zuwa ranar karshe.

Ga Yadda Zaka Sa Kwakwaluwar Mace Ya Cika Da Tunanin Ka:Tsangayar malam tonga :Ba muna cewa mata basa son kudi bane, ko ...
08/05/2025

Ga Yadda Zaka Sa Kwakwaluwar Mace Ya Cika Da Tunanin Ka:

Tsangayar malam tonga :

Ba muna cewa mata basa son kudi bane, ko basa son namiji mai kudi. Domin rayuwar mace gaba dayanta na kashe kudi ne, don haka idan mace ta zabi mai kudi akan mara shi ba laifi tayi ba.
Sai dai ba k**ar yadda mutane suke daukan cewa babu abunda zaka yiwa mace ta soka ko ka shiga ranta irin ka bata kudi, ka rika bata kudi, kana kashe mata kudi. Wannan ba haka yake ba, idan tana da kudin fa?

Yana da kyau muma fahimci cewa, mace idan tana sonka kudinka bai cika damunta ba, sai idan ya zama dole babu yadda ta iya take tambayar ka.

Ga wasu abubuwan da zaka yiwa mace ta kasance a kullum cikin Kaunar ka da tunanin ka.

Wani abunda ke sa mace ta rika tunanin namiji tana jin sa a ranta shine yadda namiji zai rika nunawa duniya yana sonta.

Idan har kaga mace na boyeka bata son a san kuna soyayya, ko ta rika hanaka bayyana son da kake mata ga wasu, ba sonka take ba.

Idan mace na sonka so take taji kuma taga kana kururu ta son da kake mata. Kana alfahari da ita a gaban kowa. Wannan yana san mace ta rika tunanin ka.

Mace tafi son kulawa ga wanda take so fiye da kudi. Idan mace tana sonka, tana so ka rika bata lokaci domin tabbatar da wannan soyayyar da kake mata.
Sai dai kuma yanada kyau ka zama baka hada soyayya da lokacin aiki ko kasuwanci.

Domin ita mace bata damu ka bar duk wani abunda kake yi ka zo mata ba a lokacin da ta bukaci hakan. Don haka ka tsara mata lokutan da zata bukace ka idan ta k**a kamin lokutan da kake zuwa wajen ta.

Baiwa mace lokaci tabbas nasa mace ta yawaita tunanin namiji saboda yana shiga mata rai.
Barkwanci ba irin na wauta ba, nasa mace ta rika yawan tunanin wanda take so.

Mace koda mara magana ce, bata son kasancewa da namijin da bai magana. Haka nan bata son namijin da idan yaje wajenta banda wa'azi bai da hiran da yake mata na nishadi.
Mace nason taji mai sonta yana sako mata hiran da zasu sata dariya da nishadi. Hakan nasa a kullum tana son ta kasance tare d

Address

Aduwa Biyu Shamaki World Gombe
Lambe

Telephone

+2347064236129

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abdulmaleek m star posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Abdulmaleek m star:

Share

Category