17/07/2026
Haatim Al-Asammiy yace “Na yi dubi ga halittu, sai na ga kowane mutum yana da masoyi, amma idan ya isa kabarinsa masoyansa sai su rabu dashi, Ni kuma sai na sanya kyawawan ayyukana su zama masoya na, domin su kasance tare dani a cikin kabarina”.
Shaykh Ibnul Uthaimin yace “A duk lokacin da Mutum ya ke kara kusantar Allah da biyayya, Allah yana buɗe masa ƙofofin ilimi da Imani wanda bai buɗewa waninsa ba”.
Ya Allah ka Yarda damu ka sa kuma a yarda damu, ya Allah karka bamu ikon cin Amanar wanda s**a amince mana. 🤲