Manbie Dental Clinic

Manbie Dental Clinic Manbie Dental Clinic (MDC)
Quality dental care for all ages 🦷
📍 Kwanar Dangora, Tudun Wada Rd, Kano
✨ Your Smile, Our Priority!

EID MUBARAK 🤍A wannan rana mai albarka, ina taya al’ummar Musulmi murnar Sallah.Allah ya karɓi ibadunmu, ya sanya mana a...
29/05/2026

EID MUBARAK 🤍

A wannan rana mai albarka, ina taya al’ummar Musulmi murnar Sallah.

Allah ya karɓi ibadunmu, ya sanya mana albarka, zaman lafiya da cigaba a rayuwa.

Sallah ba kawai sutura da shagali ba ce…

lokaci ne na nuna ƙauna, yafiya da haɗin kai tsakanin al’umma.

A matsayina na CEO, ina fatan wannan Eid zai zo mana da sababbin nasarori, lafiya da kwanciyar hankali ga kowa.

Eid Mubarak 🌙
CEO,Rdt Bello Hayatu Umar

Ba kowane aiki ake gani ba… amma ana jin tasirinsa.Duk murmushin da muka dawo da shi, duk ciwon da muka rage—shaida ne n...
01/05/2026

Ba kowane aiki ake gani ba… amma ana jin tasirinsa.

Duk murmushin da muka dawo da shi, duk ciwon da muka rage—shaida ne na jajircewar ma’aikata masu sadaukarwa.

A matsayina na CEO, ina alfahari da duk wanda ke tsayawa kowace rana domin kula da lafiyar mutane.

Ku ne ainihin dalilin da yasa muke ci gaba.
Happy Workers’ Day 👨‍⚕️

Rdt Bello Hayatu Umar
CEO, Manbie Dental Clinic

Me yasa muka zabi suna Manbie?”Wasu daga cikin ku suna tambaya…Menene ma’anar Manbie?Manbie ba kawai suna bane… alama ce...
29/04/2026

Me yasa muka zabi suna Manbie?”

Wasu daga cikin ku suna tambaya…
Menene ma’anar Manbie?

Manbie ba kawai suna bane… alama ce.

An samo shi ne daga:
Man + Bello = Manbie

👉 Man – yana wakiltar mutane, al’umma, da duk wanda yake bukatar kulawar lafiya
👉 Bello – asali ne, suna na wanda ya kafa wannan tafiya

Mun hada su ne domin mu gina suna da ke nufin:

hidima ga mutane, tare da kwarewa da kulawa mai inganci.

A gare mu:
Manbie yana nufin amincewa, kulawa, da ingantacciyar lafiyar baki.

Ba kawai clinic bane…
wuri ne da murmushi ke samun kulawa ta gaskiya.

Manbie Dental Clinic(MDC)
Your Smile, Our Priority

Manbie Dental ClinicYour Smile,Our Priority 🦷
25/04/2026

Manbie Dental Clinic
Your Smile,Our Priority 🦷

A matsayina na wanda yake jagorantar Manbie Dental Clinic, ina ganin yana da matuƙar muhimmanci mu gyara fahimtar da ake...
23/04/2026

A matsayina na wanda yake jagorantar Manbie Dental Clinic, ina ganin yana da matuƙar muhimmanci mu gyara fahimtar da ake yi game da lafiyar hakoran yara.

Akwai kuskure da dama da iyaye ke yi, musamman tunanin cewa hakoran yara ba su da muhimmanci domin za su zube. Wannan ra’ayi ba daidai ba ne.

Hakoran yara su ne ginshiƙin lafiyar baki na gaba. Idan aka yi sakaci da su, hakan na iya haifar da ciwo, matsalar cin abinci, lalacewar hakora na dindindin, har ma da tasiri ga magana da ci gaban yaro.

A nan Manbie Dental Clinic, muna karfafa iyaye da su:
– Kula da tsaftar bakin yara tun daga ƙuruciya

– Rage yawan abinci mai zaƙi da abin sha mai sugar

– Horar da yara amfani da brush da toothpaste yadda ya dace

– Kai yara duba hakora akai-akai, ba sai sun ji ciwo ba

Jagoranci na gaskiya shi ne kare lafiyar al’umma ta hanyar ilimi da wayar da kai.
Mu tuna: kula da hakoran yara yau, kariya ce ga lafiyarsu gobe.

Idan kuma bukatar karin bayani ko duba lafiyar hakoran yaronka, ƙofar mu a buɗe take.

Rdt Bello Hayatu Umar

A wasu lokuta iyaye kan ga sabon haƙori yana fitowa a bayan ko kusa da tsohon haƙorin yaro amma tsohon bai zube ba. Wann...
23/04/2026

A wasu lokuta iyaye kan ga sabon haƙori yana fitowa a bayan ko kusa da tsohon haƙorin yaro amma tsohon bai zube ba. Wannan ana kiransa(Delay Exfoliation of Primary Teeth).

Idan ba a kula da wuri ba, zai iya haifar da:
• Cunkoson haƙora (crowding)
• Matsalar tsari na haƙora
• Wahalar tsaftace baki yadda ya kamata
• Matsalar cizo (bite problems)

Abin da ya kamata iyaye su yi:
**Ku duba bakin yaro akai-akai daga shekara 5–7

**Idan sabon haƙori ya fara fitowa amma tsohon bai motsa ba, ku kai yaro dental clinic

**Kada a bar matsalar har ta jawo karkacewar haƙoran dindindin

A mafi yawan lokuta, cire haƙorin yara da bai zube ba da wuri yana taimakawa sabon haƙori ya fito daidai.

A Manbie Dental Clinic muna karɓar yara domin duba lafiyar haƙoransu da wuri, domin kare su daga matsalolin tsari na gaba.

Your Smile, Our Priority 🦷
Rdt Bello Hayatu Umar

Ka/ki na fama da warin baki (Mouth Odor)? 🦷Ka/ki sani cewa warin baki yana da manyan dalilai guda 3:1️⃣ Matsaloli daga c...
22/04/2026

Ka/ki na fama da warin baki (Mouth Odor)? 🦷

Ka/ki sani cewa warin baki yana da manyan dalilai guda 3:

1️⃣ Matsaloli daga cikin baki
Kamar datti a hakori, cutar dasashi, ko datti a harshe.

2️⃣ Matsaloli daga wasu sassan jiki
Kamar makogwaro, hanci, ko wasu cututtuka na ciki.

3️⃣ Wani lokaci mutum yana tunanin yana da warin baki alhali babu shi.

Abu mafi muhimmanci shi ne:
Kar ka yi shiru da wannan matsala.

A mafi yawan lokuta, ana magance warin baki cikin sauƙi idan an gano dalilinsa da wuri.

📍 Ka/ki ziyarci Asibitin Hakori domin duba lafiyar bakinku 🦷

Manbie Dental Clinic
Your Smile, Our Priority

Address

Tudun Wada Road Kafin Maiyaki
Kano
711105

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Manbie Dental Clinic posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share