Albani Zaria

Albani Zaria Domin Tunatarwa, Ilimi Da Gyaran Rayuwa Bisa Al-Qur’ani Da Sunnah.

Allahu akbar Tsarki ya tabbata ga allah 'Yar TikTok ta mutu, an ce an kasa shiga wayarta domin a goge account ɗinta? Shi...
08/07/2026

Allahu akbar Tsarki ya tabbata ga allah

'Yar TikTok ta mutu, an ce an kasa shiga wayarta domin a goge account ɗinta? Shin me ya sa sai an goge account ɗinta? Su waɗanda suke son a goge account ɗin, me ya sa tun tana raye ba su hana ta ba? Ashe sun san laifi take aikatawa s**a ƙyale ta, sai yanzu bayan ta mutu suke son kuma a goge TikTok ɗinta? Idan an goge TikTok din, ya za a yi da sauran videos ɗinta da ke yawo a shafukan wasu kuma?

Wannan matashi sunansa M***i Yaks shi ma ɗan TikTok ne. Ya rasu tun 31 ga watan Mayu, 2024. Yau kusan shekaru 2 kenan, amma ba a taɓa jin an ce ana ƙoƙarin goge TikTok account ɗinsa ba. Allah Ya jikansa da rahama.

Wannan ya k**ata ya zama wa'azi garemu, ya 'yan uwa. Mu san abubuwan da za mu dinga yadawa a wannan kafa ta social media, kar sai mun mutu a riƙa ƙoƙarin goge accounts ɗinmu.

Sheikh Malam Ba Cima Zaune BaneMalam Dr Alakali Abubakar Salihu Zarai kenan yayin da yake yin feshi da kan shi a wata go...
08/07/2026

Sheikh Malam Ba Cima Zaune Bane
Malam Dr Alakali Abubakar Salihu Zarai kenan yayin da yake yin feshi da kan shi a wata gonar sa ta bayan gida.

Daman ko a cikin wa’azi idan magana ta k**a, malam yakan sanar da mutane cewa shi fah ba cima zaune bane, yanada sana’ar sa, ko kuma ma nace yanada sana’o’in shi.
Har kullum muna yi masa fatan alkhairi da samun nasara a rayuwa

Allah ya Kara Basira Da Lafiya Mallam Allah ya Bawa Kasarmu Zaman Lafiya Amin🤲

08/07/2026

Halinda Nigeria take ciki
ayau🧏😥 Part (7)

07/07/2026

Halinda Nigeria take ciki
ayau🧏😥 Part (6)

🚨JININ SHEIKH JA'AFAR.•Malam Jafar ya mutu amma kuma ya bar baya mai kyau, kuma inshaAllah yanzu haka yana karɓar sak**a...
07/07/2026

🚨JININ SHEIKH JA'AFAR.

•Malam Jafar ya mutu amma kuma ya bar baya mai kyau, kuma inshaAllah yanzu haka yana karɓar sak**akon tarbiyyar da yayiwa yaran sa, k**ar yadda Hadisi yayi ishara.

•Na saurari wani Jawabi da Mahaifiyar Malama Zainab tayi a lokacin rufe Tafsirin da take yi na Azumi, bayanai ne tayi cike da godiyar Allah da kuma bayyanar da Alfahari ƙarara akan baiwar da Allah yayi mata na bata Malama Zainab a matsayin 'yar ta.

•Ba shakka idan ka kalli rayuwar Malama Zainab zaka yi buri kaima ace 'yar ka tana a irin ƙadamin ta, domin rayuwa ce mai cike da ilimi, Tarbiyya haɗi da Dattako, to wa zai ƙi irin wanna 'yar?.

•Ba iyayen Malama Zainab ba kaɗai, duk wani masoyin karatu yana Alfahari da ita, haka duk wata Mace a Nigeria tana fatan ta kasance k**ar ta a ilimi da Tarbiyya.

Allah ya ƙarawa rayuwar ta Albarka Ameen.

✍️ Been Muhammad

07/07/2026

Halinda Nigeria take ciki
ayau🧏😥 Part (5)

Wallahi Wannan ba musulinci baneSUBHANALLAH 😭 ALLAH KA MANA TSARI DA SHI,A👇A ganina abin da na gani a wannan jana'izar y...
06/07/2026

Wallahi Wannan ba musulinci bane

SUBHANALLAH 😭
ALLAH KA MANA TSARI DA SHI,A👇

A ganina abin da na gani a wannan jana'izar ya sa na yi mamaki matuƙa.

Na duba abin ta fuskar abin da na sani daga koyarwar Musulunci, ban san inda aka koyar da irin wannan tsari na jana'iza a cikin Alƙur'ani ko Sahihun Hadisai ba

Ina da tambaya ga masu wannan fahimta
A ina ne hujjar yin irin wannan jana'iza take a Musulunci?

Kuma mene ne bambancin wannan tsari da wasu manyan jana'izo na shugabannin addinai da ake yi a wasu ƙasashe?

Idan akwai hujja daga Alƙur'ani ko ingantacciyar Sunnah, a kawo ta cikin ladabi da ilimi domin a amfana. Allah Ya shirye mu zuwa ga gaskiya, Ya sa mu riƙe abin da ya tabbata daga Littafinsa da Sunnar Annabinsa ﷺ

Ku tambayi ma'abota sani idan ba ku sani ba Suratun An-Nahl 43

06/07/2026

Halinda Nigeria take ciki
ayau🧏😥 Part (4)

06/07/2026

Sheikh Ja'afar one said
👂👇

Shin ka san mutumin da bai yi karatun Jami'a ba,amma ya koyar da masu neman shedar karatun  digirin gigirgir (PhD) a Jam...
05/07/2026

Shin ka san mutumin da bai yi karatun Jami'a ba,amma ya koyar da masu neman shedar karatun digirin gigirgir (PhD) a Jami'ar duniya??

Sheikh Muhammad Nasiruddin Al-Albani (wanda aka fi sani da Sheikh Albani) yana daya daga cikin manyan malaman hadisi mafiya fice a karni na 20

Sheikh Albani bai taba yin karatun digiri (B.A, M.A, ko Ph.D) a kowace jami'a ba. Duk da haka, saboda zurfin iliminsa na hadisi, Jami'ar Musulunci ta Madina (Islamic University of Madinah) ta gayyace shi ya koyar da ilimin hadisi a matakin farfesa daga shekarar 1961 zuwa 1963. Shi ne ma ya tsara manhajar koyar da ilimin hadisi ta jami'ar a wancan lokacin

A shekarar 1999, an karrama Sheikh Albani da lambar yabo mafi daraja a duniyar Musulmi, wato King Faisal International Prize saboda hidimar da ya yi wa Musulunci (Specifically for Islamic Studies). Abin ban sha'awa shi ne, bayan an bashi kyautar kudi mai yawa tare da lambar yabon, bai rike kudin ba; ya bayar da duka kudin kyautar ga dakin karatun Jami'ar Musulunci ta Madina.

Sheikh Albani ya rasu a ranar 2 ga Oktoba, 1999 a birnin Amman na kasar Jordan yana da shekaru 85. Kafin rasuwarsa, ya bar wasiyya mai tsauri cewa:

- A binne shi da sauri (cikin sa'o'i kadan bayan rasuwarsa).

- Kada a sanar da mutane da yawa domin kada taron mutane ya jinkirta binne shi.

- Ba ya son kuka mai sauti ko kuma yabo na wuce kima a kansa.

An cika masa wannan wasiyya, inda aka binne shi cikin sa'o'i hudu kacal da rasuwarsa, kuma mutane kalilan ne s**a halarci jana'izar, duk da cewa shi babban malami ne na duniya.

Rahimahullah 🤲🤲🤲

Address

Dorayi
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Albani Zaria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share