19/08/2024
YANZU- YANZU: Shugaba Tinubu ya amince a biya tallafin Man Fetur.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da buƙatar da kamfanin mai na ƙasa, NNPC ya aike masa ta dawo da tallafin man fetur.
Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito kamfanin man na ƙasa NNPC na bayyana hakan a yau Litinin, biyo bayan ɗaukan dukkan matakan da s**a dace.
Matakan sun haɗa da ƙara yawan man da ake samarwa ta hanyar yaƙi da masu satar man da lalata shi, da biyan basuss**a gami da haɓaka cinikayyar man, da sauransu.