Tsalle daya

Tsalle daya in here you find what you need. the swag is for all.

31/07/2026

Rarara new song

Wannan shine mutun na farko da aka fara yiwa alluran rigakafi
24/07/2026

Wannan shine mutun na farko da aka fara yiwa alluran rigakafi

23/07/2026
Tsalle daya,
23/07/2026

Tsalle daya,

Babbar magana!! Wasu kwararru a jami'ar Bonn da ke Jamus sun gano cewa shan tabar Wiwi na kara inganta lafiyar tsofaffi....
17/01/2026

Babbar magana!! Wasu kwararru a jami'ar Bonn da ke Jamus sun gano cewa shan tabar Wiwi na kara inganta lafiyar tsofaffi.

Tawagar karkashin jagorancin Andras Beilke-Gorzo ta gano cewar zukar tabar Wiwi ka iya takaita saurin tsufan kwakwalwa idan har wadanda s**a manyanta suna sha

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce, gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen ci gaba da bujiro da sabbin matakai...
01/01/2026

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce, gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen ci gaba da bujiro da sabbin matakai da tsare-tsaren da zasu bunkasa tattalin arzikin kasar.

TSALLE DAYA°

Da dumi dumi ta.Kungiyar kwallon kafa ta birtania, (chelsea) ta sallami managan ta Enzo maresca.
01/01/2026

Da dumi dumi ta.

Kungiyar kwallon kafa ta birtania, (chelsea) ta sallami managan ta Enzo maresca.

NAWA NE HARAJIN? Hukumar tattara harajin ta tarayya wato FIRS, wadda yanzu ta koma Nigeria Revenue Service wato NRS, a k...
01/01/2026

NAWA NE HARAJIN?

Hukumar tattara harajin ta tarayya wato FIRS, wadda yanzu ta koma Nigeria Revenue Service wato NRS, a kundin da ta fitar ta nuna cewa kasancewarku ƴan Najeriya ba shi ne zai sa ku biya harajin ba illa dai yawan samun da kuke yi, inda ta saka sharaɗin da sai mutum ya kai zai fara biyan haraji.

Babu haraji a kan N800,000 ta farko
N2,200,000 za a biya kaso 15 na kuɗin
N9,000,000 za a biya kaso 18 na kuɗin
N13,000,000 za a biya kaso 21 na kuɗin
N25,000,000 za a biya kaso 23 na kuɗin
N50,000,000 za a biya kaso 25 na kudin

JERIN MUTANE DA ABUBUWAN DA AKA DAUKE WA HARAJI.

Bisa kundin hukumar tattara harajin ta Najeriya, an ɗauke harajin daga kan wasu kuɗade da mutane kamar haka:

Mutumin da ke samun kuɗi daidai da albashin ma'aikacin Najeriya mafi ƙanƙanta na N72,000, a wata.
Mutumin da samunsa a shekara bai wuce N1,200,000 ba.
Kyauta (babu haraji a kyauta).
Kuɗin da mutum ke tarawa na fansho.
Kuɗin fansho da garatuti.
Kuɗin insorar lafiya.
Asusun lamunin gidaje.
Riba a kan kuɗaɗen rance na mutumin da ke cikin gida yake son ya malleke shi.
Kuɗaɗen insora.
Kuɗin sallamar ma'aikaci daga aiki da ba su wuce N50,000,000 ba.
Kuɗin da aka sayar da gidan da aka ma'aikaci ya mallaka bayan shekaru yana zaune a ciki.
Kuɗin da mutum ya sayar da wata kadara da bai wuce N5,000,000 ba.
Sayar da motoci na ƙashin kai da ba su wuce biyu a shekara ba.
Riba a kan hannun jarin da ba ta kai N150,000,000 a shekara ko kuma N10,000,000.
Kuɗaɗen jinƙai da na ƙungiyoyin addini (waɗanda ba don riba aka kafa su ba)
Ƙananan masana'antu da uwar kuɗin jarinsu ba ta wuce N100,000,000 ba ko kuma gabaɗaya jarin bai wuce N250,000,000.
Ƙananan ƴan kasuwa da suke tasawa

A ranar 1 ga watan Janairun 2026 ne ake sa ran sabuwar dokar haraji ta Najeriya za ta fara aiki wadda shugaba Bola Ahmed...
01/01/2026

A ranar 1 ga watan Janairun 2026 ne ake sa ran sabuwar dokar haraji ta Najeriya za ta fara aiki wadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya saka wa hannu domin amincewa ta zama doka.

An dai ta tunanin cewa za a dakatar da fara aiwatar da harajin kafin sabuwar shekara sakamakon zarge-zargen cushe da aka yi wa dokar ta haraji, wadda aka ce ta bambanta da asalin wadda majalisar dokoki ƙasar ta amince da ita.

A ranar 30 ga watan Disambar 2025 ne shugaba Tinubu ya sanar da cewa babu buƙatar dakatar da fara aiwatar da harajin domin hakan zai katse wa Najeriya burinta na samar da cigaban da ake buƙata.

Sai dai ya ce yana sane da irin zarge-zargen da ake yi dangane da cushe a dokar kuma yana aiki da majalisar dokokin ƙasar wajen samar da mafita.

Yanzu dai abin da al'ummar Najeriyar ke son sani shi ne ta yaya wannan haraji zai shafe su daga ranar 1 ga watan Janirun sabuwar shekarar 2026? BBC ta yi nazarin dokar harajin ga kuma bayanan da ta tattara.

Address

Minna
Minna
920101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tsalle daya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category